Shahararren Mawakin Yarabawa, Olanrewaju Adepoju, Ya Rasu

Olarewaju Adepoju
Olarewaju Adepoju

Shahararren mawaƙin Yarabawa, kuma marubuci, Olanrewaju Adepoju ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Ya rasu ne da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Lahadi a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo.

Ɗansa, Adejare Adepoju ne ya sanar da rasuwarsa a yammacin Lahadi.

Wasu daga cikin wakokinsa sun hada da Sagba Dewe, Ironu Akewi, Orirun Yoruba, da sauransu.

A zamanin mulkin Soja, Adepoju ya kasance mai karfin gaske domin yawancin wakokinsa sun ta’allaka ne kan gyara matsalolin al’umma da manufofin gwamnati marasa kyau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here