Rundunar ‘Yan Sandan kasa (NPF) ta musanta wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke nuna wani jami’in ‘yan sanda yana hulda da ’yan bindiga a kan babura a Jihar Katsina, in da ta bayyana cewa labarin na karya ne da yaudara ga jama’a.
A cikin wata sanarwa da aka raba wa ‘yan jarida a ranar Laraba, rundunar ta bayyana cewa mutanen da aka gani a bidiyon ba ‘yan bindiga ba ne, membobin Kungiyar ‘Yan Banga ta Kasa (VGN) da masu farauta da aka yi wa rajista da ke tallafawa ayyukan tsaro da ake yi ne a wasu sassan jihar.
Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu ya sanya wa hannu, ta ce masu aiki sa kai ne da ke aiki tare da hukumomin tsaro a kananan hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina.
“Rundunar ’Yan Sandan ta Kasa a ta musanta labarin karya da yaudara a bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta, wanda ke zargin cewa an ga jami’in ‘yan sanda yana hulda da ’yan bindiga a Jihar Katsina,” in ji sanarwar.
Rundunar ta bayyana cewa bidiyon kawai ya nuna alaka ta yau da kullun tsakanin jami’i da masu sa kai na tsaron al’umma da suka fita zuwa wani wuri domin aiki a matsayin wani bangare na kokarin magance ayyukan laifuka da inganta tsaron jama’a.
“Don kauce wa rashin fahimta, mutanen da aka gani a bidiyon ba ’yan bindiga ba ne. Membobi ne na Kungiyar ’Yan Banga ta Kasa (VGN) da masu farauta wadanda ke da rajista da aka amince da su, da ke tallafawa ayyukan tsaro da ake yi a halin yanzu tare da hukumomin tsaro a kananan hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina,” in ji sanarwar.
Ta jaddada cewa duk wani zargin cewa jami’in yana hulda da ’yan bindiga “karya ce kawai, da mugunta suke, kuma an yi shi ne domin yaudarar jama’a.”
’Yan sanda sun yi alla wadai da abin da suka bayyana a matsayin karkatar da gaskiya da yada bayanan karya da zai iya haifar da firgici a tsakanin jama’a, ya raunana amincewa da hukumomin tsaro da kuma hana ayyukan tsaro da ake yi.
“Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta la’anci gaba ɗaya karkatar da gaskiya da yaɗa bayanan karya da zai iya haifar da firgici a tsakanin jama’a, ya raunana amincewa da hukumomin tsaro, da kuma hana ayyukan tsaro da ake yi,” in ji sanarwar.
Rundunar ta bukaci ’yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin da aka yada a bidiyon, su dogara kawai ga bayanan da suka fito daga rundunar ’yan sanda na hukuma da kuma majiyoyin gwamnati masu izini, tare da gargadin mutane da kungiyoyin da ke kirƙira, buga ko yada bayanan karya da za su iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro.
“Rundunar ta gargadi mutane da kungiyoyin da ke kirkira, bugawa ko yada bayanan karya da za su iya cutar da zaman lafiya da tsaron jama’a,” in ji sanarwar.
Ta kuma jaddada aniyarta na kare tsaron jama’a, inda ta ce za ta ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaron al’umma da aka amincewa da sauran abokan hulda da suka dace wajen yaki da laifuka a fadin kasar.













































