Rundunar ‘yan sandan ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da sashin amsa korafe-korafen ta, a hedikwatar rundunar domin kai rahoton rashin da’a na jami’anta.
Shugaban sashin, El-Musta Sani, babban Sufeton ‘yan sanda ne ya yi wannan roko a wajen wani taron koli da hukumar korafe-korafen jama’a (PCC) tare da hadin gwiwar gidauniyar karfafa matasa da tabbatar da adalci a zamantakewa ta shirya a Abuja.
Mista Sani, ya ce an samar da sashin ne a shekarar 2015 domin gudanar da korafe-korafe kan jami’an ‘yan sanda daga jama’a.
Karin labari: “Dalilin da yasa na saka Bam a Masallaci” – Wanda ake Tuhuma a Kano
Ya ce, ya zuwa yanzu, daga rubu’in farko na shekarar 2024, rundunar ta samu korafe-korafe 459 daga jama’a kan jami’anta da maza, ta kafafen sada zumunta na zamani.
Ya kuma bayyana cewa an warware 265 daga cikin kararrakin yayin da 195 ke hannun ‘yan sanda.
A cewarsa, “yana ɗaukar sashin kwanaki 21 don karba da kuma kammala bincike kan dukkan korafe-korafe”.
Ya ce abin damuwa ne yadda jama’a ba su san hanyoyin da za a bi wajen gabatar da kokensu ba.
Karin labari: EFCC ta gurfanar da Emefiele a kotu bisa laifin buga takardun kudi
“Babban matsalar ita ce cibiyoyin suna nan, amma ‘yan Najeriya ba su san ayyukansu ba.
“Muna samun korafe-korafe ta hanyar WhatsApp, daTwitter, da kiran waya da kuma shigar da kara.
“Kuma sashin yana da alhakin kai tsaye ga ofishin babban sufeton ‘yan sanda ta hannun jami’in hulda da jama’a,” in ji shi.
Karin labari: Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ta sake yin barazana ga gwamnatin tarayya
Mista Sani ya bada tabbacin kara wayar da kan jama’a domin su yi amfani da damar da suka samu wajen gabatar da kokensu domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
A nasa jawabin, babban kwamishinan PCC, Abimbola Ayo-Yusuf, ya jaddada bukatar karfafa cibiyoyin yaki da rashin adalci da cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa, ci gaban da aka samu yadda ya kamata, shi ne mabudin gudanar da shugabanci nagari, inda ya ce taron na da nufin inganta harkokin hidima da kuma tabbatar da ‘yancin yin korafi da tada zaune tsaye ga kowa.
Karin labari: Emefiele ya ce bashi da laifi kan buga bayanan kudi na Naira Miliyan 684 da Biliyan 18.96
Shi ma da yake jawabi, Maurice Okoye, Babban Jami’in Hukumar Jewel Social Empowerment Initiative, ya ce akwai matukar bukatar kulawa da sakamakon da ake bukata wajen magance al’amura a Najeriya.
Mista Okoye ya bayyana rashin gudanar da sakamakon a matsayin babban kalubale, wanda ke haifar da rashin bin diddigi a tsakanin shugabannin hukumomin gwamnati.
Mista Okoye ya yi kira da a maido da amincewar jama’a kan tsarin shari’a tare da jaddada bukatar yin riko da rikon amana a tsakanin shugabanni.