Masu shaidar rigakafin Corona ne kadai zasu shiga sansani-NYSC

nysc2 1
nysc2 1

Hukumar yi wa ka hidima NYSC ta ce daga yanzu sai wanda suke da shaidar yin allurar rigakafin Corona ne kadai zasu shiga sansanonin daukar horo na hukamar.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, inda aka jiyo shugaban NYSC Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim yana cewa matakin zai fara aiki ne daga lokacin shiga sansanin horarwa mai zuwa nan da ‘yan makonni.

Janar Shuaibu Ibrahim ya ce daga yanzu sai masu yi wa ƙasa hidima wato sun nuna katin shaidar rigakafin kafin su shiga sansani, inda ya gargaɗe matasa masu hidimar kasa su  daina yin balaguro cikin dare saboda tsaro, tare da bin sauran matakan kare kai da ta fuskar tsaro da Hukumar ta tanadar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here