Jam’iyyar (APC) ta lashe zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da aka gudanar a mazabun Ungogo da Kano Municipal.
A mazabar Kano Municipal, ɗan takarar APC, Aliyu Nabil Daneji, ya samu ƙuri’u 7,484 inda ya yi nasara tare da wakiltar mazabar a Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Ibrahim Tajo Siraj, ne ya sanar da sakamakon tare da ayyana Daneji a matsayin wanda ya yi nasara.
Haka kuma a mazabar Ungogo, ɗan takarar APC, Aminu Sa’ad Sa’ad, ya samu ƙuri’u 8,975 inda ya lashe kujerar.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen na mazabar, Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, ya ayyana Sa’ad a matsayin wanda aka zaɓa.
idan za a iya tunawa cewa manyan jam’iyyun adawa da suka haɗa da (NNPP), (PDP) da (ADC) ba su shiga zaɓen ba.
Sai dai an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓen.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Ambasada Abdu Zango, ya danganta ƙarancin fitowar da lokacin gudanar da zaɓen da kuma ƙarancin jam’iyyun da suka shiga takara.
Ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana, duk da ƙarancin halartar masu kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe da dama.
Guraben sun zama babu kowa ne bayan rasuwar ’yan majalisar da ke wakiltar mazabun Ungogo, Aminu Sa’ad, da Kano Municipal, Sarki Aliyu Daneji, waɗanda suka rasu a rana guda.
Sabbin waɗanda suka yi nasara a zaɓen ’ya’yan marigaya ne, wato Aminu Sa’ad Sa’ad a Ungogo da Aliyu Nabil Daneji a Kano Municipal.













































