Gwamnan Kano ya bukaci NBC ta tsara ka’idoji da sanya ido kan kafafen watsa labarai na intanet

Abba Kabir Yusuf sad 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci hukumar kula da kafafen yaɗa Labarai ta Kasa (NBC) ta tsara ka’idoji da sanya ido kan gidajen rediyo da talabijin na intanet domin dakile yaduwar labarai marasa inganci da ke tada hankula.

Tun farkon mulkin sa a 2023, wasu mataimakan gwamna sun kai ‘yan jarida hudu ofishin ‘yan sanda, yayin da akalla biyu aka kai su kotu saboda zargin cin mutunci ta kafafen intanet.

A baya, kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya, ya tuhumi jaridar Kano Times da editan ta Buhari Abba da wasu biyu, yayin da Darakta janar na shirye-shiryen gwamna ya kai Daily Nigerian da ma’aikacinsa Audu Umar ofishin ‘yan sanda, sannan ya shigar da kara a kotu.

Haka zalika, a watan Oktoba 2024, gwamnati ta janye takardar dakatarwa ta ‘yan jarida 14 da ke aikin daukar rahoto a fadar gwamnati, ciki har da NTA, AIT, FRCN da Freedom Radio, sai dai dukkannin zarge-zargen daga baya ana yin watsi da su.

Gwamna Yusuf ya nuna damuwa kan yadda wasu kafafen intanet ke yada labarai masu rabuwar kai kan addini da siyasa, wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.

Ya bukaci NBC ta tabbatar da bin ka’idoji da inganci a kafafen dijital domin hana yada bayanan karya da kalaman tsangwama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here