Kotun Ƙoli ta tabbatar da shugabancin David Mark na ADC

IMG 20260430 WA0022

 

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari’a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari’ar da ake yi.

Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake da cire sunan shugabancin ADC ɓangaren David Mark daga shafin INEC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here