Kungiyar masu gidan burodi za su soma yajin aikin gama gari

Burodi, kungiya, masu, gidan, yajin aiki, najeriya
Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya AMBCN, ta bayyana janye yajin aikin da ta shiga bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami'an ma'aikatar noma ta...

Ƙungiyar masu gidan burodi ta AMBCN, ta yi barazanar shiga yajin aikin gama-gari daga ranar 27 ga watan Fabrairu saboda rashin kyawun yanayin kasuwanci.

Shugaban ƙungiyar ta ƙasa reshen jihar Kogi, Chief Adeniyi Bamidele Gabriel ne ya bayyana haka ranar Talata a birnin Lokoja lokacin wani taron manema labarai.

Ya ce sanarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Alhaji Mansur Umar da sakataren ƙungiyar ta ƙasa, Mista Jude Okafor suka fitar.

Karanta wannan: “Sukar da Trump ya yi kan Nato abin kunya ne” – Biden

Ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara rufe shaguna saboda tsadar farashin kayan da suke amfani da shi wajen yin burodi kamar fulawa da sukari da yis da man ƙuli da man fetur da kuma dizel duk ta dalilin cire tallafin mai da kuma rashin daidaito a kasuwar canjin kuɗade da yawan haraji ta hannun hukumomin gwamnati.

Ƙungiyar dai ta nemi a dakatar da duk wasu nau’ikan haraji a kan masu sana’ar gasa burodi a matakan tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here