El-Rufai ya janye karar take hakkin dan Adam da bukatar diyyar Naira Biliyan 1 kan alkalin kotun majistare na Abuja

Nasir El Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Talata ya janye karar da ya shigar kan take hakkokinsa na dan Adam a gaban kotu, wadda ya yi kan wani babban alkalin kotun majistare a Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka saka a matsayin wanda ake kara na biyu a cikin shari’ar Naira Biliyan 1.

Lauyan sa, Ugochukwu Nnakwu, ya sanar da mai shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke Abuja wannan mataki, jim kadan bayan an kira karar domin sauraron bukatarsa ta gaggawa a kotu.

Matakin janye karar ya biyo bayan abin da mai shari’ar ta lura da shi a zaman da ya gabata, inda ta nuna cewa karar ba ta fayyace sunan alkalin majistaren da aka kai kara ba, duk da cewa an saka shi a matsayin wanda ake kara na biyu.

Bayan sake zaman kotu, lauyan ya bayyana cewa an shirya sauraron bukatar su ta ba da izinin isar da takardun kotu ta wata hanya ta musamman ga alkalin, amma daga baya ya ce sun shigar da wata bukata ta janye karar gaba daya a kansa.

Ya roki kotu da ta cire sunan alkalin daga cikin wadanda ake kara, tare da soke bukatar da suka gabatar a baya, abin da lauyoyin Hukumar ICPC, ‘yan sanda, da kuma ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ba su nuna adawa da shi ba.

A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Abdulmalik ta amince da bukatar, inda ta cire sunan alkalin daga cikin karar tare da soke bukatar da aka gabatar a baya, sannan ta dage shari’ar domin bai wa lauyan damar gyara sauran karar.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya nuna cewa Nasir El-Rufai na neman diyyar Naira Biliyan 1 daga Hukumar ICPC, babban alkalin majistare na Abuja, sufeton ‘yan sanda na kasa, da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya kan zargin take hakkokinsa.

A cikin karar, ya bukaci kotu ta ayyana cewa bincike da aka kai gidansa da kuma sammacin bincike da aka bayar sun saba wa kundin tsarin mulki, tare da neman a hana amfani da duk wata hujja da aka samu daga binciken, sannan a dawo masa da kayayyakin da aka kwace daga gidansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here