Shugaban Ghana John Mahama da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da sauran manyan shugabannin Afrika za su halarci taron tattaunawar dimokuraɗiyya na gidauniyar Goodluck Jonathan (GJF) da za a gudanar a Accra, Ghana, ranar 17 ga Satumba, 2025.
Mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara na musamman, Ikechukwu Eze, ya bayyana cewa taron zai haɗa da kwararrun masana ci gaban duniya da kuma fitattun shugabanni daga nahiyar.
Cikin wadanda ake sa ran halarta akwai Jonathan kansa, Kadré Ouédraogo tsohon Firaministan Burkina Faso da tsohon shugaban hukumar ECOWAS, da kuma shugaban hukumar ta yanzu, Dr. Omar Alieu Touray.
Haka kuma, mai girma Bishop Matthew Hassan Kukah na Katolikan Sokoto zai kasance babban mai gabatar da jawabi, yayin da Obasanjo zai jagoranci zaman taron.
Taken taron na bana shi ne: “Dalilan Da Suke Kassara Dimokuraɗiyya” wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin Ghana.
Eze ya ce taron zai ba mahalarta damar yin nazari kan cigaba, ƙalubale da kuma damar da tsarin dimokuraɗiyya ya kawo a yankin yammacin Afrika tsawon shekaru.
Tun daga shekarar 2021 aka fara gudanar da wannan tattaunawa a kowace shekara domin zurfafa bincike kan dorewar dimokuraɗiyya da tasirinta ga rayuwar al’umma.
A shekarar 2024, jigon tattaunawar ya ta’allaka ne kan ilimi mai ma’ana, inda aka gayyato Prof. Olubayi Olubayi daga Kenya wanda ya yi kira da a samar da manyan jami’o’i na bincike da gasa don habaka ci gaban fasaha a nahiyar.
A cewar Eze, ana sa ran Bishop Kukah da sauran masana a taron bana za su yi tsokaci mai zurfi kan hanyoyin da za a dakile koma-baya da kuma lalacewar ka’idoji da dokokin dimokuraɗiyya a kasashen Afrika.
NAN













































