Kotun Amurka ta yanke wa tsohon Janar Manaja na kamfanin NNPC hukunci kan cin hancin Dala Miliyan 2.1

Paulinus Okoronkwo

Kotun tarayya a Amurka ta samu Paulinus Okoronkwo, ɗan asalin Najeriya wanda kuma ɗan ƙasa ne na Amurka, bisa laifin karɓar cin hanci na dala miliyan 2.1.

Okoronkwo ya taɓa rike matsayin babban manaja a sashen kamfanin NNPC, wanda yanzu ya koma NNPC Limited.

Lauyoyin gwamnati sun bayyana cewa Okoronkwo ya yi amfani da matsayinsa wajen karɓar kuɗin cin hanci daga kamfanin Addax Petroleum, reshen kamfanin kasar China, Sinopec, domin ba su damar samun damarmaki na hakar mai mai fa’ida a Najeriya.

An bayyana kuɗin a matsayin kudin “taimakon lauya” amma hakikanin gaskiya cin hanci ne.

Shaidu sun nuna cewa shugabannin Addax sun canza bayanai a cikin takardu, sun sallami ma’aikata da suka nuna damuwa, sannan suka ba da bayanan karya ga masu duba harkokinsu.

Karin karatu: Majalisar Dattawa ta bai wa NNPCL makonni 3 ya bata bahasi kan wasu kuɗi Tiriliyan 210

A watan Oktoba 2015 ne aka aika kuɗin zuwa asusun amana na ofishin lauyansa da ke Los Angeles.

Rahotanni sun ƙara da cewa daga cikin kuɗin, kusan dala miliyan 1 ya yi amfani da shi wajen biyan kuɗin gidan da ya saya a Valencia, California, amma bai bayyana kuɗin a cikin bayanin harajin da ya kai wa gwamnati na shekarar 2015 ba.

Bugu da ƙari, a shekarar 2022, Okoronkwo ya yaudari jami’an binciken tarayya ta hanyar musanta amfani da kuɗin wajen sayen gida, tare da ikirarin cewa kuɗin amana ne na abokan cinikinsa.

Mai shari’a John Walter ya dage zaman yanke hukunci zuwa ranar 1 ga watan Disamba, inda Okoronkwo ke fuskantar yiwuwar dauri na shekaru 10 a kurkuku kan kowanne daga cikin laifukan wanke kuɗi da kuma tangarda wajen shari’a, da kuma shekaru 5 kan laifin kaucewa biyan haraji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here