Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce babu gwamnan jihar da zai zo ya rushe sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kawo a jihar.
Ganduje ya bayyana cewa Allah ba zai kawo gwamnan da zai rusa sabbin masarautun ba, wadanda ya bayyana a matsayin alamar ci gaba da hadin kai da kuma zaman lafiyar Jihar Kano.
“Ina tabbatar muku babu abin da zai kawar da su da izinin Allah har zuwa karshen duniya.
“Mai niyyar rusa su kuma Allah Ba zai kawo shi jihar Kano ba, kuma muna tabbatar muku cewa an yi wadannan masarautu ne domin ku da kuma ci gabanku.
“Muna rokon Allah, ko mun bar mulki, Ya kare wadanna masarautu daga sharri,” in ji Ganduje.
Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na NNPP ya kuma yi tsokaci kan sabbin masarautu hudu da Ganduje ya kafa, a matasyin abin da ya kamata Gwamnatin Abba Kabir Yusuf mai jiran gado ta duba.
Madugun Kwakwasiyyan ya yi tsokacin ne bayan ce-ce-ku-cen da ya karade kafofin sanda zumunta cewa gwamnatin Abba za ta dawo da Sarki Sanusi II a kan kujerarsa, ta kuma hade masa Masarautar Kano kamar yadda take kafin Ganduje ya tube shi.
Sanusi II wanda ke dasawa da Kwankwaso, ya yi ta samun samun takun saka ga Gwamnatin Ganduje, har daga karshe ta tube masa rawani.
Sai dai yayin jawabinsa a taron Ranar Ma’aikata a jihar, Ganduje ya ce, Allah Ba zai jarabi Jihar Kano da gwamnan da zai rusa masarautun ba.
Ya bayyana wa taron ma’aikatan cewa “Duk wanda ya je hedikwatar wadannan masarautu zai shaida cewa mun kawo musu ci gaba.
“wadannan masarautu an kirkiro su saboda hadin kai da ci gaba da tarihi da kuma farfado da darajar al’addu da kuma daga darajar wadannan yankuna,” in ji shi.
(Aminiya)













































