“Fasa rumbunan ajiye abinci babban laifi ne” – Minista

kayan abinci, rumbuna, minista, fasa, ajiye
Ƙaramar ministar Abuja ta bayyana ayyukan fasa rumbun ajiye abinci da wasu mutane suka yi a birnin da cewa babban laifi ne. Dakta Mariya Mahmoud ta bayyana...

Ƙaramar ministar Abuja ta bayyana ayyukan fasa rumbun ajiye abinci da wasu mutane suka yi a birnin da cewa babban laifi ne.

Dakta Mariya Mahmoud ta bayyana hakan ne bayan kai ziyarar gani da ido don shaida irin ɓarnar da aka yi a wajen ajiye abincin da aka tatuke.

Karin labari: ‘Yan sanda sun haramta amfani da POS ko taransifa a ofisoshinsu

A shafinta na X ta wallafa cewa: “Na je rumbun ajiye abinci a Gwagwa-Tasha don tantance irin ɓarnar da zauna-gari-banza suka yi a ranar Lahadi. Wannan abin ya wuce yunwa, babban laifi ne!!!

Abin da na gani abu ne mara daɗi, yanayi ne da wasu zauna gari banza suka wawushe duka hatsain da sauran kayan abinci da ke wurin.

Karin labari: “Abinda yasa na dawo shugabancin hukumar Hisbah” – Sheikh Daurawa

Wani ɗan kasuwan da BBC ta zanta da shi a unguwar karmo da ke birnin, ya bayyana cewa mutane sun wawashe masa kayan abinci a wurin ajiyar kayan da ke Karmo.

Mutumin ya ce lamarin da ya faru a ranar Lahadi, ya janyo masa asarar sama da naira miliyan 100.

Yayin da mutanen da ke maƙwaftaka da wurin suka bayyana yadda masu fasa rumbun suka zo da makamai da suka haɗa da adduna da sanduna da wuƙaƙe wajen fasa rumbun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here