
Shugaban hukumar agajin gaggawa na Majlisar Ɗinkin Duniya a Gaza, ya yi korafin cewa suna fuskantar ƙarancin kayan agaji da gangan da nufin kawo karshen aikin hukumar a Gaza.
Philippe Lazzarini ya shaidawa zauren MDD a birnin New York cewa ana yaɗa bayanan ƙarya kan hukumar ga masu ba da agajin da hukumar ke tafiyar da aikinta da shi.
Karin labari: “Fasa rumbunan ajiye abinci babban laifi ne” – Minista
Mista Lazzarini ya ƙara da cewa dagula ayyukan hukumar zai haddasa durƙushewar ayyukan jin kai a Gaza.
Ya ce yin hakan tamkar mun sadaukar da ɗaukacin al’ummar yaran da aka samar a tushen kiyayya da tashin hankali nan gaba.
Isra’ila ta gagara yin cikakken bayani kan zargin da ta yi wa hukumar a watan Junairu, na hannun jami’anta 11 a harin da Hamas ta kaddamar ga Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktobar bara.












































