Shugaban hukumar Hisba na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da cewa ayyukan hukumar za su ci gaba da gudana kamar yadda aka fara na gangamin kauda badala da tsarkake jihar daga bata gari.
Malam Daurawa ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan sulhu tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf.
Sheikh Daurawa ya sanar da yin murabus din ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan kalaman da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kalubalanci yadda hukumar Hisbar ke gudanar da ayyukanta.
Karin labari: Yanzu-yanzu: An sasanta tsakanin sheikh Daurawa da gwamna Abba
Bayan janye murabus ɗinsa, Daurawa ya ce shaidan ne ya shiga tsakani “an kawar da shaidan a tsakani an kuma fahimci juna kan manufar ayyukan hukumar da gwamna na jihar Kano, wannan sabani tamkar taki ya karawa hukumar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ba su kudaden tafiyar da ayyukan ci gaba da gyaran tarbiyya a jihar.
Shehin malamin ya ce gwamnati ba ta karbi takardar murabus dinsa ba, a yanzu kuma sun fahimci juna.
Karin labari: PDP ta saka ranar zaben fitar da gwani na gwamna a Ondo
“Gwamna ya roke ni da na ci gaba da zuwa ofis, ya yi alkawarin ba mu hadin kai dari bisa dari, kuma yanzu haka na dawo bakin aikin shugabancin hukumar Hisba Insha Allahu,” in ji Daurawa.
A karshe Sheikh Daurawa ya gargadi masu yada bidiyoyin badala a shafukan sada zumunta da su kuka da kansu, ko dai su tuba su daina ko kuwa dai su bar jihar Kano.