Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kano ta Arewa sun sake jaddada kudirinsu na samar da kuri’u masu yawa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin a zaben gama gari na 2027.
Sun bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na APC na Kano ta Arewa da Sanata Barau ya kira ranar Asabar a Kano, inda shugabannin jam’iyya, zababbun jami’ai da ‘yan siyasa na kasa suka hallara domin karfafa hadin kai da tsara dabarun tunkarar zabe mai zuwa.
A wata sanarwa da Mai Bai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Malam Ismail Mudashir ya fitar, ta rawaito Barau yana cewa taron na da nufin karfafa hadin kai a cikin gida da kuma tabbatar da Kano ta Arewa a matsayin sansanin APC a jihar Kano.
A cewar Barau sun hada kai kuma suna maida hankali, Kano ta Arewa za ta tsaya tsayin daka wajen marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf baya.
Ya kara da cewa da yardar Allah za su samar da kuri’u masu rinjaye ga Shugaba Tinubu, Gwamna Abba da sauran ‘yan takarar APC a zabe mai zuwa.
Sanarwar ta ce Barau ya sanar da bayar da motoci 26 da babura 141 ga shugabanni, mataimakan shugabanni, kansiloli da sakatarori a kananan hukumomi 13 na Kano ta Arewa. Shugabanni da mataimakansu za su samu motoci, yayin da kansiloli da sakatarori za su samu babura.
Barau ya ce bai wa shugabannin tushe kayan aiki da damar zirga-zirga na da muhimmanci wajen karfafa hadin kai, wayar da kai da janyo kuri’u gabanin 2027.
Ya bukaci ‘yan jam’iyya su ajiye sabanin da suka gabata su hada kai domin cimma burin bai daya.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, Hon. Tijjani Abdulkadir Jobe, ya sake tabbatar da shirinsu na marawa Shugaba Tinubu da Gwamna Abba baya domin wa’adi na biyu.
Shugaban karamar hukumar Danbatta, Hon. Jamilu Danbatta, wanda ya yi magana a madadin shugabannin kananan hukumomi 13, ya gode wa Barau bisa tallafin da ya bayar, yana mai cewa za su ba shi cikakken goyon baya.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Muhammad Bello Butu-Butu, ya ce Kano ta Arewa ba ta taba samun sanata mai kokari kamar Barau ba.
Taron ya samu halartar kwamishinoni, ‘yan majalisun kasa da na jiha, shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka kammala da alkawarin yin aiki tukuru domin sake zaben Shugaba Tinubu, Sanata Barau da Gwamna Abba a 2027.













































