Gwamnan Kano ya sauke Buba Galadima daga shugabancin Majalisar Gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Kano

Buba Galadima 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Injiniya Buba Galadima daga mukamin Shugaban Majalisar Gudanarwar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano.

Wannan na cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da nadin Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin sabon Shugaban Majalisar Gudanarwar makarantar.

Matakin sauke Galadima ya biyo bayan sake fasalin majalisar da daidaita ta da manufar Kano First Agenda.

Sanarwar ta ce duk da cewa wa’adin Majalisar Gudanarwar shekaru uku ne, an dakatar da nadin shugaban kafin cikar wa’adin sakamakon gyare-gyaren da ake yi domin inganta aikin kwalejin.

Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga Injiniya Buba Galadima bisa gudunmawar da ya bayar ga makarantar a lokacin da yake shugaba.

Ya kuma bukaci sabon shugaban, Sarkin Gaya, da ya yi amfani da kwarewa da jagorancinsa wajen daga darajar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano ta fuskar karatu da gudanarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here