Wata gobara ta tashi a Gidan Gilas, wanda aka fi sani da “Gidan Mai,” a kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano, inda ta lalata kayayyaki na Miliyoyin Naira.
Wani shago da aka fi sani da sayar da kayan masarufi ya kama da wuta, yayin da hayaki mai kauri ya turnuke sararin sama, lamarin da ya jawo dimbin ‘yan kasuwa da mazauna yankin suna kokarin ceto kayayyaki tare da hana wutar bazuwa zuwa sauran gine-gine.
Shaidun gani da ido sun ce wutar na ci gaba da bazuwa zuwa wasu shaguna da gine-gine, abin da ya kara tayar da hankula a kasuwar mai cunkoso.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano sun isa wurin da motar kashe gobara, amma ruwan ya kare yayin da suke kokarin shawo kan wutar.
Daga baya wata motar kashe gobara ta isa domin ci gaba da kokarin kashe wutar.
Wata motar dakon ruwa ta kamfanin Aspira Nigeria Limited ta isa wurin domin taimakawa wajen kashe gobarar.
Sai dai ‘yan kasuwa da mazauna yankin sun nuna damuwa cewa ana bukatar karin tankokin ruwa domin shawo kan wutar gaba daya tare da hana karin asara.
Lamarin ya biyo bayan wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar ta Singa makonnin da suka gabata, wadda ta jawo asara mai yawa ga ‘yan kasuwa.













































