Ana zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan

zanga-zanga, Ibadan, tsadar rayuwa
Dubban mutane sun hau kan titunan Ibadan na jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa a Najeriya. Zanga-zangar ta...

Dubban mutane sun hau kan titunan Ibadan na jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya domin nuna fushinsu kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Zanga-zangar ta fara ne daga yankin Mokola ta birnin, inda masu yin tattakin suka yi mahaɗa.

Hakan na zuwa ne bayan gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohin Kano da Neja, inda mutane da dama suka fito domin kokawa kan matsalar tashin farashin kayan masarufi.

Karanta wannan: “Anyi kuskuren kama motocin simintinmu a Adamawa” – Kamfanin Dangote

Al’umma a Najeriya na fama da matsalar tashin kayan masarufi ne tun bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, jim kaɗan bayan ratsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Tun daga wancan lokacin ne farashin wasu kayan masarufi da abinci da sufuri suka nunka, lamarin da ya ƙara jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali.

Karanta wannan: Mu Yi Sadaukarwa Domin Ci Gaba Da Hadin Kan Nijeriya – Sarkin Gwandu

Tun farko rundunar ‘ƴansanda a jihar Oyo ta gargaɗi masu zanga-zangar da su kaucewa duk wani abu da zai tayar da hankalin al’umma kuma ta bayyana cewa za ta tsaurara tsaro domin ganin lamarin bai rikiɗe zuwa tarzoma ba.

Gwamnatin Najeriya dai ta bayyana cewa tana yin duk abin da ya kamata wajen sauƙaƙa wa al’umma halin matsin na rayuwa, inda ta ayyana wani shiri na tallafin kayan abinci da na masarufi ga al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here