“Anyi kuskuren kama motocin simintinmu a Adamawa” – Kamfanin Dangote

Motar, Dangote, Adamawa, kamfani
Hukumomin kamfanin siminti na Dangote sun bayyana cewa an sako wasu manyan motocin su guda biyu da aka kama a jihar Adamawa bisa kuskure. Kamfanin ya bayyana...

Hukumomin kamfanin siminti na Dangote sun bayyana cewa an sako wasu manyan motocin su guda biyu da aka kama a jihar Adamawa bisa kuskure.

Kamfanin ya bayyana cewa manyan motocin biyu dauke da buhunan siminti 900 kowanne daga kamfanin siminti na Obajana suna kan hanyarsu ta zuwa Jamtari na karamar hukumar Maiha a jihar Adamawa bisa zuwa wajen abokin cinikayya.

Sai dai jami’an tsaro sun tare su inda suka zarge su da kokarin fitar da haramtattun kayayyaki zuwa jamhuriyar Kamaru ta hanyoyin Adamawa.

Karanta wannan: Sojojin ruwan Maroko sun ceto baƙin haure ƴan Afirka 141

Lamarin ya afku a ranar Juma’ar da ta gabata cikin watan Fabrairu biyo bayan umarnin zartarwa na hana safarar abinci da kayayyakin gini a kan iyakokin kasar nan ta hanyar Adamawa da gwamnatin jihar Adamawa ta yi.

Wata sanarwa dauke da sa hannun babban jami’in kula da sa hannun jari da sadarwa na kungiyar Mista Anthony Chiejina, ta bayyana cewa kamfanin na da kamfanin siminti mai aiki a kasar kamaru kuma, zargin yunkurin fitar da siminti a can karya ne da kuma mugun nufi.

Karanta wannan: Kamfanin X ya amince zai biya tsoffin ma’aikatansa na Ghana

Sanarwar ta bayyana cewa manyan motocin guda biyu suna kan hanyarsu ta kai kayayyakin da wani abokin ciniki ya nema, kuma suna mamakin dalilin da ya sa jami’an tsaro za su kutsa kai tare da zarge su da yunkurin karkatar da kayansu zuwa Jamhuriyar Kamaru.

Ya kara da cewa, “Abin mamaki ne a kan hanyarsu ta kai kayayyakin zuwa adireshin da aka bayyana, jami’an tsaro da ke wannan hanyar sun kama su a wani kauye mai suna Wurolabi.”

Karanta wannan: Mu Yi Sadaukarwa Domin Ci Gaba Da Hadin Kan Nijeriya – Sarkin Gwandu

Sanarwar ta ce jami’an da suka yi kamen sun dage cewa motocin na karkata akalarsu ne tunda da alamun ba su kula da cikakken bayanin abin da aka rubuta a kan hanyar Waybill ba. Kamfanin ya ce direbobin biyu sun yi kokarin yi wa sojojin bayani amma abin ya ci tura.

Ya kara da cewa, “Bayan haka jami’an namu sun samu gayyata daga hukumar DSS ta jihar Adamawa, kuma mun bayyana musu hakikanin matsayinsu.

Sai da muka nuna musu bin diddigin motocin daga DCP Obajana har zuwa karshe da sojoji suka kama su, domin tabbatar musu da cewa motocin ba su ketare zuwa jamhuriyar Kamaru ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke bayyanawa cikin rashin sani.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here