Masu neman Fasfo sun zargi jami’an kula da shige da fice da karbar kudaden da suka wuce kima

Passports
Passports

Wasu ‘yan Najeriya da ke bukatar yin fasfo na kasa da kasa sun zargi jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa dake ofishin fasfo na birnin tarayya Abuja da karbar kudaden da suka wuce kima a wajen su.

Masu korafin sun ce duk da umarnin da Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya baiwa hukumar a baya-bayan nan cewa a gagauta tsaftace tsarin, amma har kawo yanzu babu abin da ya sauya.

Masu neman yin fasfo din da suka yi magana da Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, sun koka kan yadda jami’an hukumar kula da shige da ficen suka sanya su biyan wasu makudan kudade kafin samun takardar iznin tafiya kasashen ketare.

Wasu daga cikinsu sun yi zargin cewa bayan da aka kammala aikin fasfo din su, sai da suka kara biyan wani kudin har Naira dubu biyar (5,000) kafin a basu fasfo din.

Malam Ahmed Isa, wani ma’aikacin gwamnati ne ya ce ya je ofishin yin fasfo din har sau 10 kuma har yanzu bai samu ba, duk da cewa ya cika duk ka’idoji.

Shi kuma Mohammed Umar, ya ce ofishin ne da nufin a sake yi masa fasfo din da ya kare amma jami’in hukumar kula da shige da ficen suka ce sai biya Karin wasu kudaden bayan na ka’ida.

Wata mata da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ta yi rasa wani muhimmin horo a kasar waje sakamakon gaza ba ta fasfo din ta duk da kuwa ta biya kudin yin fasfo din gaba daya.

Wani dan jarida, Dennis Abraham, wanda fasfo dinsa ya kare a watan Agusta, ya ce bayan ya biya kudin fasfo din har Naira dubu dari da ashirin (120,000) wanda zai kai tsawon shekaru 10 kafin ya kare, da farko an ce masa ya biya karin Naira dubu ashirin da biyar (25,000) daga bisani kuma aka ce ya kara biyan wata Naira dubu goma sha biyar (15,000) wai don a gyara kuskuren kwanan watan haihuwarsa.

Wata mata ita ma da ta nemi a sakaya sunanta, t ace tun a watan Agustan shekarar 2022 ta shigar da bukatar a sabunta mata fasfo din ta ta kafar Internet amma har yanzu tana nan tana jira.

Blessing Ibiyemi, ta shaidawa kamfanin dillacin labarai NAN cewa duk da ta bi duka ka’idojin da ake bukata amma an jami’an sun gaza bat a Fasfo dinta, lamarin daya yi sanadiyyar rasa gurbin karatun ta a kasar waje.

Wani jami’in hukumar kula da shige da fice da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai NAN cewa tsarin ya samu tazgaro da yawa, inda ya kara da cewa wadanda suka nemi fasfo ta kafar Internet ba lallai su sami na su ba.

Wani jami’in shima ya shaidawa kamfanin dillancin labaran na Nijeriya NAN cewa zarge-zargen da al’umma ke yi game da matsalolin da gaske ne, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, da kuma babbar barazana ga tsaron kasa.

Jami’in, ya kuma ba da shawarar cewa dole ne a dauki tsauraran matakai don dakile matsalar, inda ya bukaci mutane da su kauracewa duk wani yunkuri na tilasta musu ba da cin hanci domin a yi musu fasfo.

Sai dai mai Magana da yawun hukumar, Dr Adedotun Aridegbe, ya musanta zargin, yana mai cewa wasu dake son bata sunan hukumar kula da shige da fice ta kasa, ne suka kirkiri labarin marar tushe.

A cewarsa, babu yadda za a yi wadanda za’a yi wa Fasfo su biya fiye da adadin kuɗin da ake biya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here