Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta bukaci mabobinta da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin daukar matakin daya kamata a fadin kasar matukar ba a saki shugaban kungiyar da aka kama ba zuwa daren Larabar nan.
Idan dai za a iya tunawa, an kama Joe Ajaero ne a Owerri babban birnin jihar Imo da safiyar ranar Laraba 1 ga watan Nuwambar nan da muke ciki, yayin wata zanga-zangar da ma’aikata suka yi a jihar Imo kan zargin cin zarafi da kuma kin biyansu albashi da gwamnatin jihar ta yi.
Wasu ‘yan sanda dauke da makamai a Owerri ne suka kama Shugaban na NLC a Sakatariyar kungiyar ta NLC, suka kuma tafi da shi wani waje da ba’a kai ga gano wa ba.
Sai dai a wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fitar jim kadan bayan kama Ajaero, sun zargi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma da kwamishinan ‘yan sandan jihar, cewa sun yi garkuwa da shugaban kungiyar ta NLC.
Kungiyar ta NLC dai ta bukaci mambobinta da su kasance cikin shiri domin daukar matakin gaggawa, domin a cewarta ma’aikata ba za su iya ci gaba da zuwa aiki ba yayin da Shugabanta ke tsare a wani waje.
Kungiyar ta kuma bukaci Shugaba Bola Tinubu kan cewa ya umarci gwamnan jihar ta Imo Uzodimma ya aje aniyarsa ta mayar da jihar sansanin ‘yan daba da masu zubar da jini.