Gwamnatin tarayya ta ce za ta sanya takunkumi ga gidajen rediyon Birtaniya (BBC) da jaridar Daily Trust, mai wallafa sashen Hausa na Aminiya kan shirin da suka tattara kan ta’addanci da barnar ‘yan bindiga a Najeriya a kwanan nan.
Lai Mohammad, ministan yada labarai da al’adu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, The Cable ta ruwaito.
A kwanan nan ne wasu fafa-fayan bidiyo suka yadu a kafafen sada zumunta, inda ake nuna wakilan BBC da na Aminiya suna hira da ‘yan ta’adda a cikin dazukan da asuke fake.
“Ina mai tabbatar muku, ba za su tsira da wannan aiki na kambama ta’addanci da ‘yan bindiga ba a Najeriya. “Lokacin da wasu kafafe masu daraja irin su BBC ke ba wa ‘yan ta’adda kafafensu, suna nuna fuskokinsu kamar su taurarin Nollywood ne… Ina so in tabbatar musu da cewa ba za su yi tsira ba, za a sanya takunkumin da ya dace a kansu. “Abin da zan iya cewa shi ne akwai wata hukuma mai kula da harkokin yada labarai ta Najeriya (NBC) kuma suna sane da wadannan abubuwan da suka faru kuma suna duban wane bangare na ka’idojin yada labarai ne BBC da Daily Trust suka karya.”
Hakazalila, bidiyon ya nuna yadda karuwar satar mutane ke ta’azzara, da kuma yadda rashin tsaro a Zamfara ya faro ta rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Fulani. A watan Maris din bana, Daily Trust/Aminiya, ya buga rahoto na musamman da shirin da ya bankado manyan batutuwan da suka shafi ‘yan bindiga a Najeriya. An yi hira da ‘yan ta’addan da suka addabi Arewa irinsu Bello Turji dai dai sauransu.
Bello Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, sanannen kasurgumin ‘yan bindiga ne da ke addabar Arewacin Najeriya, musamman jihohin Zamfara, Sokoto da Neja.













































