Tinubu ya amince da sauyawa wasu gidajen yari 29 matsuguni 

tinubu 2 (2)

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauyawa wasu gidajen ajiya da gyaran hali guda 29 matsuguni a fadin kasar nan.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da kananan motoci kirar Green Maria guda 39 da kuma rumfunan gadin harsashi guda biyar a hedikwatar hukumar da ke kula da gidajen yari (NCoS) da ke Abuja ranar Juma’a.

Ya ce, wasu gidajen yarin sun haura shekaru 100, don haka a yanzu ba za su iya tsare fursunonin ba.

Karanta: Gwamnatin tarayya ta amince da daukar likitoci 50, ma’aikatan jinya 100 a gidajen yari

Da yake jawabi tun da farko, Konturola Janar na hukumar kula da gidajen yarin kasar nan Sylvester Ndidi Nwakuche, ya ce motocin aiki guda 39 da aka sayo an yi su ne don isar da fursunoni cikin aminci da inganci zuwa da kuma dawowa daga kotuna, yana mai tabbatar da cewa za a rarraba su zuwa gidajen yarin da suke da jaramcinsu.

Tun daga ranar Litinin 17 ga Fabrairu 2025, akwai jimillar fursunoni dubu 80,066, kuma acikin wannan adadin guda dubu 53,225 suna jiran hukunci, yayin da ragowar dubu 26,841 ne kadai aka yankewa hukuncin daurin shekaru daban-daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here