Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 50 da ma’aikatan jinya 100 aiki don magance bukatun lafiyar fursunonin a cibiyoyin gyaran hali da tarbiyya na kasar nan.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan, inda ya kuma bayyana cewa, hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) za ta tura likitocin zuwa cibiyoyin gyaran daurarru domin gudanar da aikinsu na shekarar hidimar su, tare da jaddada muhimmancin kiyaye hakkin marasa galihu a cikin al’umma.
Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai, Alao Babatunde, ya fitar ranar Alhamis.
Karanta: Tinubu ya amince da shekaru 65 na wa’adin ajiye aikin likitoci da ma’aikatan lafiya
Ministan ya kuma bayyana cewa, za a ba wa ma’aikatan jinya da ke cikin hukumar kula da lafiyar Ma’aikata (NCoS) damar tsawaita ayyukansu fiye da shekarun ritayar da aka saba yi domin shawo kan matsalar karancin ma’aikata na wucin gadi.
Idan dai za a iya tunawa, kafin a nada Tunji-Ojo a matsayin Ministan harkokin cikin gida, Jihohi irinsu Ribas sun fuskanci gagarumin gibi a bangaren ma’aikatan jinya don kula da fursunonin, wanda ke nuna bukatar magancewa.