Ranar Ma’aikata: Ma’aikata da dama sun rasa rayukansu a hadarin mota a Kwara

Kwara map 750x430

Ma’aikatan lafiya da dama sun rasa rayukansu ranar Juma’a a wani mummunan hadarin mota da ya auku a kan hanyar Oke-Onigbin zuwa OmuAran yayin da suke dawowa daga Taron Ranar Ma’aikata na shekarar 2026 da aka gudanar a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su, mambobi ne na Kungiyar Ma’aikatan Kiwon Lafiya ta Kasa (MHWUN) a Karamar Hukumar Ekiti, an ruwaito suna kan hanyarsu ta komawa gida ne bayan halartar bikin Ranar Ma’aikata na shekara-shekara da aka yi a filin wasa na Jihar Kwara da ke Ilorin lokacin da mummunan hadarin ya faru.

Ko da yake ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu ba, shaidun gani da ido sun ce hadarin ya faru da yamma bayan da tayar motar daya daga cikin motocin da ke dauke da mambobin kungiyar ta fashe, wanda ya sa direban ya rasa yadda zai sarrafa ta har ya kai ga mummunan hadari.

Da yake jawabi, Shugaban karamar hukumar Ekiti, Awelewa Olawale Gabriel, ya bayyana lamarin a matsayin babban rasara ga karamar hukumar a bangaren kiwon lafiya, da jihar baki daya.

“Zukatammu sun yi nauyi. Wadannan ƙwararrun ma’aikata ne da suka bar gidajensu don murnar martabar ƙwadago, sai kawai suka gamu da wannan mummunan ƙaddara a hanyarsu ta dawowa.

“Mun rasa ‘yan kishin kasa wadanda suka yi wa al’ummarmu hidima da tausayi da jajircewa,” in ji shi cikin bakin ciki.

Ya ce mummunan lamarin ya jefa su cikin bakin duhu lokacin ya kamata ya zama na hadin kai da murna ga ma’aikatan Najeriya, ya kuma kara da cewa wadanda lamarin ya shafa sun mutu ne suna hidima ga bil’adama.

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayuwar ta su da kuma daukacin al’ummar MHWUN, yana addu’ar neman rahamar Allah ga rayukan mamatan da kuma karfin hali ga wadanda suka rage.

Wasu daga cikin mambobin kungiyar da lamarin ya rutsa da su, suna ci gaba da karbar magani a halin yanzu.

Ko da yake ba a tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukannasu ba a hukumance ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, lamarin ya jefa karamar hukumar da al’ummar ma’aikata cikin alhini.

Domin nuna alheni ga wannan rash in, MHWUN reshen Jihar Kwara ta ayyana kwanaki uku na jimami, tare da umurci mambobi a faɗldin jihar da su rage tutar kungiyar zuwa rabin sanda don girmama abokan aikinsu da suka rasu.

Shugaban karamar hukumar ya kuma tabbatar da cewa karamar hukumar za ta yi aiki tare da Gwamnatin Jihar Kwara da sauran hukumomin da abin ya shafa don ba da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma taimakawa wajen biyan kudin jinya na wadanda suka jikkata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here