Dan Buhari ya samu tikitin APC kai tsaye don neman kujerar Majalisar Wakilai

Yusuf Buhari

Yusuf Buhari, da ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya karbi tikitin tsaya wa takarar neman kujerar Dan Majalisar Wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Daura/Sandamu/Mai’adua a jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Yusuf ya samu tikitin ne ba tare da hamayya ba bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Talata 28 ga watan Afrilu a Katsina, inda suka amince da shi baki daya a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Shugaban Kwamitin yarjejeniya na ganin Daura, Alhaji Ahmed Dangiwa, tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, ne ya sanar da yarjejeniyar.

Da yake magana bayan amincewa da Yusuf, Shugaban APC na Karamar Hukumar Mai’adua, Mannir Musa, ya bukaci mambobin jam’iyyar da su karbi sakamakon cikin kyakkyawan fata.

“Ina rokon dukkan al’ummarmu da su kasance masu biyayya kuma su karbi shawarwarin da kwamitin da masu ruwa da tsaki suka cimma cikin kyakkyawan fata. Ya kamata mu yi aiki tare don hadin kai da ci gaban jam’iyya da al’ummarmu,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnan Katsina Dikko Radda da ya tallafa wa masu neman takara wadanda ba su samu tikiti ba domin su ci gaba da yi wa al’ummarsu hidima.

Shugaban ya bukaci masu neman takara da aka ba su tikiti ta hanyar yarjejeniya da su yi wa kananan hukumominsu aiki idan an zabe su a babban zabe mai zuwa.

Yusuf Buhari, a jawabinsa, ya gode wa mambobin jam’iyyar bisa yardar da suka ba shi kuma ya yi alkawarin samar da kyakkyawar wakilci idan an zabe shi. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here