Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin shekarun ritaya ga likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya daga shekaru 60 zuwa 65.
Sakataren yada labarai na kasa na kungiyar likitocin Najeriya (NMA), Dr Mannir Bature shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Legas.
Sanarwar ta ce an umurci ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Pate da ya gabatar da amincewar a hukumance ga ofishin shugaban ma’aikata domin fara aiwatawa.
Labari mai alaƙa: NMA: ta umarci likitocin asibitin yara na Hasiya Bayero da su janye ayyukansu saboda rashin tsaro a Kano
Sanarwar ta ce taron ya kuma samu halartar shugabannin kungiyar likitoci da likitan hakora ta Najeriya (MDCAN), kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM), da kuma hadin gwiwar kungiyoyin kiwon lafiya (JOHESU).
Amincewar ta sa, ta biyo bayan ce tattaunawa da kuma ci gaban da aka samu dangane da jin dadin likitoci da sauran kwararrun masana kiwon lafiya a Najeriya.
A cewar sanarwar, ministan ya tabbatar da cewa basussukan da kungiyar ke bi bayan daidaita tsarin albashin likitocin (CONMESS) an sanya su cikin tsarin biya nan ba da jimawa ba.