Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar nan Kayode Egbetokun, ya bukaci majalisar dattijai da ta rika gudanar da bincike a kan bacewar bindigogi a sirri saboda dalilai na tsaro.
Egbetokun ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Alhamis.
Ya yabawa kokarin majalisar dattijai na gudanar da cikakken bincike kan bacewar bindigogin.
Labari mai alaƙa: Majalisar dattijai ta sanar da bacewar bindigogi sama da 3,900
“Mun yaba da binciken da kwamitin majalisar dattijai ya yi kan bacewar bindigogi.
“Muna kira ga kwamitin da ya gudanar da zaman tattaunawa a nan gaba kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tsaro ta hanyar daukar hoto domin kada a haifar da mummunar fahimta a zukatan ‘yan Najeriya da kuma a zukatan kasashen duniya.
Sufeto-janar na ‘yan sandan ya bayyana kudurin sa na ci gaba da hada karfi da karfe da majalisar dokokin kasar nan domin samar da sauye-sauye masu kyau a kasar da inganta rayuwar ‘yan Najeriya da kuma tsaron kasa.
Akpabio, bayan karanta wasikar, ya ce wasikar IGP ta fito karara, yana mai cewa “yana magana ne da kan sa.”
Ya ce yayin da ‘yan sanda za su gudanar da bincike a cikin gida, majalisar dattawa kuma za ta ci gaba da gudanar da bincikenta. (NAN)