Kwamitin kula da harkokin jama’a na majalisar dattawa ya nuna matukar damuwa kan batutuwa da dama da suka shafi rundunar ‘yan sandan Najeriya, da suka hada da badakalar kudi da kuma bacewar bindigogi.
A yayin nazarin rahoton Odita-Janar, an sanar da ‘yan majalisar kan laifuka takwas da aka rubuta a kan ‘yan sanda da suka hada da badakalar kwangilar da ta kai Naira biliyan 1.136, da kuma bacewar bindigogi sama da 3,900 da suka hada da bindigogin AK-47, wadanda ake fargabar suna hannun ‘yan ta’adda.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda Abdul Suleiman, ya tabbatar wa ‘yan majalisar cewa ‘yan sanda sun amsa tambayoyin tantancewa yadda ya dace.
Lamarin dai ya ta’azzara ne a lokacin da Sanata Ningi ya kira taron zartarwa domin tattauna lamarin a asirce daga bisani ya fice daga taron.
Duk da haka, shugaban kwamitin ya dage cewa mataimakin sufeton yan sanda ya bayyana inda makaman da suka bace suke, yana mai cewa batun yana da muhimmanci a kasa.
Labari mai alaƙa: Sufeton ƴan sandan Najeriya ya haramtawa ‘yan sanda daukar bindiga cikin fararen kaya
“‘Yan sanda ba za su bari wadannan makamai su bace ko ta halin kaka ba, amma wannan batu ne na tsaro da aka fi tattauna shi a sirri,” in ji shi.
Sai dai kuma mafi yawan ‘yan majalisar sun dage a kan a yi wa al’umma adalci. Wasu Sanatoci da suka hada da Sanata Victor Umeh da Sanata Joel Onawakpo-Thomas sun goyi bayan shugaban majalisar, inda suka nuna rashin amincewa da kiran da aka yi na a yi zaman sirri.
Sanata Victor Umeh ya soki hukumar ‘yan sanda da kasa kwato makaman da suka bace sakamakon rashin tsaro a fadin kasar nan.
Ya bayar da hujjar cewa “Dubban AK-47 sun bace a daidai lokacin da rashin tsaro ya kai kololuwa. Ya kamata ‘yan sanda su iya gano wadannan makamai. Idan sama da bindigu 3,900 ba a gano su ba, hakan na nufin tsaron mu ya lalace.
Kwamitin da ke kula da asusun gwamnati ya bayyana rashin gamsuwa da bayanin, inda ya sake kiran IGP din da ya gurfana gaban kwamitin a ranar Litinin.