An sako mutanen da aka sace a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan.
Sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga ‘yan ta’addar domin a sako su ko ba a biya su ba.
Wani mamba a kungiyar dake shiga tsakanin ‘Yan ta’addan da Iyalan wandanda aka sace din Tukur Mamu a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya ce shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.

Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani.
Mahaifin yaran hudu, Abubakar, dan tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue, Manjo Janar Idris Garba Mai ritaya ne.

‘Yan ta’addan sun kuma sako wata mata ‘yar shekara 60, Hajiya Aisha Hassan wadda aka ce an kubutar da ita ne sakamakon kalubalen rashin lafiya da ke barazana ga rayuwarta a baya-bayan nan.

Sunayen ‘yan uwa 6 da aka saki sune Abubakar Idris Garba wanda shi ne mahaifin ‘ya’yan hudu, matarsa Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10.
Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba ‘yar shekara 7 da Imran Abubakar Garba mai shekaru 5 da karamar Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.
Ya zuwa yanzu, mutane 42 ne cikin wadanda abin ya shafa saka shaki iskar ‘yanci.
Adadin wadanda har yanzu ‘Yan ta’addan ke rike da su ya kai 35.
A ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka farmaki wani jirgi, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama, lamarin da ya bayyana karara akwai lam’a game da harkar tsaron kasar nan.













































