Gwamnatin tarayya ta umurci kamfanonin sadarwa da suka hada da MTN, Globacom, Airtel, da 9mobile da su hana shigar duk wani kira daga Abokin Ciniki wadanda basu hada layukansu da lambar dan kasa ta NIN ba daga yau 4 ga Afrilu, 2022.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital Isa Pantami ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
A cewar sa, matakin wani bangare ne na aiwatar da tsarin hada NIN da SIM wanda gwamnati ta fito dashi.
Sanarwar ta samu sa hannun hadin guiwar Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Sadarwa ta Najeriya, Ikechukwu Adinde; da Shugaban Kamfanin Sadarwa na Kamfanin, Hukumar Kula da Shaida ta Kasa, Kayode Adegoke.
Gwamnatin tarayya ta umurci masu amfani da hanyoyin sadarwa da su hada layukan waya wato SIM da lambar dan kasa NIN dinsu a watan Disamba na 2020, a matsayin wani bangare na “manufofin tsaro da zamantakewa” na gwamnatin amma yawancin ‘yan Najeriya sun yi watsi da tasirin, wanda rashin yin hakan ke tallafawa masu garkuwa da mutane a sassa daban daban na kasar nan.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, Pantami ya ce ya zuwa yanzu, sama da layukan waya Miliyan 125 ne aka hada su da NIN.











































