
Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, ta saki sakamakon daliban da suka rubuta jarrabawar, ba tare da sauran dalibai ba, saboda matsala da suka ci karo da ita yayin da akai jarrabawar a fadin kasa baki daya.
JAMB ta sanar da sakin sakamakon ne a wata sanarwa da shugaban shashin kula da al-uma na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, yau Laraba a Abuja.
Benjamin ya ce hukumar ta samar da hanyoyi masu sauki yayin dubu sakamakon a shafin hakumar na yanar gizo.
“ Ya ce dalibai zasu duba sakamakon nasu ta hanyar tura sakon karta kwana “RESULT zuwa 55019”
“ Dalibai kuma zasu iya saukar da sakamakon nasu a shafin hukumar na yanar gizo” Injishi.
(NAN)












































