Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana aiki ba tare da ɓata lokaci ba domin kubutar da ɗalibai mata da aka sace a jihar Kebbi tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa a faɗin ƙasar nan.
A cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai Alhaji Mohammed Idris ya fitar a Abuja, ya ce, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dage kan cewa kare rayuwar kowane ɗan Najeriya, musamman ɗaliban makarantu, babban alhaki ne da ya rataya a kan gwamnati.
Sanarwar ta nuna takaicin harin da aka kai wa ɗaliban da kuma kashe wani jami’in makarantar da yake gudanar da aikinsa, tare da bayyana jimami ga iyalan ɗalibai mata da aka sace dagaMakarantar sakandaren Maga da ke cikin yankin Danko/Wasagu na jihar Kebbi.
Ministan ya ce, gwamnati tana da cikakken tabbacin dawo da ɗaliban cikin koshin lafiya, inda aka bai wa hukumomin tsaro da na leken asiri umarni kai tsaye da su gano inda aka kai su, su ceto su, sannan su kamo masu laifin domin fuskantar hukunci.
Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an cimma wannan buri, tare da bayyana cewa ana ƙarfafa tsarin tsaron cikin gida ta hanyar sabunta ƙarfin dakarun soja, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin hana hare-hare da hanzarta dakile barazanar tsaro idan ta taso.
A halin da ake ciki, rundunar ’yan sanda ta ƙasa tare da sojoji sun fara babban aikin bincike da ceto domin gano inda aka kai ɗaliban, inda jami’an tsaro ke bincikar hanyoyin da ’yan bindiga suka bi da dazukan da ke makwabtaka domin ceto ɗaliban tare da kama waɗanda suka aikata laifin.













































