Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa a kan Marigayi MKO Abiola wanda ake kyautata zaton ya na kan hanyar lashe zaben shugaban kasa a 1993. Punch ta rahoto Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na bayyana Mashood Kashimawo Abiola wanda ya mutu a gidan yari a matsayin ayar damukaradiyya.
Da yake magana, Shugaban kasan ya yarda mutanen Najeriya su na shan wahala a sakamakon tashin da farashin man fetur ya yi saboda janye tallafi.
Bola Tinubu yake cewa gwamnatinsa za tayi wa al’umma sakayya ta hanyar gagaruman ayyukan more rayuwa a bangarorin sufuri da ilmin zamani.
Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta maida hankali wajen samar da isasshen wutar lantarki, kiwon lafiya da sauran abubuwa na jin dadin rayuwa. Tinubu yake cewa ya fahimci wahalar da ake sha, amma ya ce ba za a dawwama a wannan hali ba, ya kara da cewa janye tallafin fetur din ya zama dole.













































