
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Musa Ille, sakataren jam’iyyar PDP mai mulki a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
An ce ‘yan ta’addan sun harbe Musa ne a kofar gidansa da ke garin Tsafe da yammacin jiya Litinin.
Karin labari: Yadda gwamnatin Najeriya ta kubutar da Mutane 1000 da aka yi garkuwa da su babu kudin fansa – NSA
Marigayi Musa Ille ya kasance dan siyasa mai kishin kasa wanda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 wanda ya samar da Dauda Lawal a matsayin gwamnan jihar.
Lamarin dai na zuwa ne ‘yan makonni bayan da aka kashe wani jigo a jam’iyyar PDP Shafi’u Abubakar tare da wasu mutane biyu a karamar hukumar Maradun.
Karin labari: TCN ta bayyana dalilan sake maido da wutar lantarki na kasa
Marigayi Shafi’u Abubakar na daya daga cikin masu neman kujerar shugaban karamar hukumar Tsafe a karkashin jam’iyyar PDP.
Karamar hukumar Tsafe dai na ci gaba da tabarbarewar ayyukan ‘yan fashi da makami a ‘yan kwanakin nan, sai dai gwamnatin ta ce ba za ta bar komai ba don ganin an dawo da zaman lafiya a duk yankunan da ake fama da rikici a fadin jihar.












































