Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bukaci a yi cikakken bincike akan lamarin da ya faru a Jihar Kaduna  

JNI 750x430
JNI 750x430

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin da ya faru a kauyen Tudun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Idan za’a iya tunawa a ranar 3 ga watan Disamba, dakarun sojojin Najeriya, suka kai hari da jirage marasa matuka a yankin lokacin da suke gudanar da Mauludi.

Sakataren kungiyar JNI, Farfesa Khalid Aliyu, a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Talata ya bukaci a yi adalci ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Aliyu ya ce JNI alhinin abin da ya faru a kauyen Tudun-Biri da ke karamar hukumar Igabi.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomi, da su gaggauta daukar matakan kula da lafiyar duk wadanda abin ya shafa tare da biyan diyar wadanda suka rasu.

A cewarsa, kiran ya zama wajibi la’akari da cewa a baya-bayan nan an samu irin wannan lamari a jihohin Yobe da Zamfara da Borno da sauran wurare.

Sakataren ya nanata kudurinsa na tabbatar da adalci da kuma tabbatar da cewa haka ba za ta sake afkuwa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here