Hukumar EFCC ta kama wani mutum da ake zargi da damfarar sama da Dala dubu 63

EFCC Operatives
EFCC Operatives

Hukumar EFCC reshen jihar Legas, ta gurfanar da wani a gaban babbar kotu da ke Ikeja bisa zargin damfarar dala dubu 63 da 599.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito cewa Abdulhamid Isah na fuskantar tuhume-tuhume uku da suka hada da samun kudi ta haramtacciyar hanya da sata da kuma zamba.

NAN ya kuma rawaito cewa wanda aka gurfanar a gaban mai shari’a Ismail Ijelu, ya ki amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

Dan sanda mai shigar da kara na EFCC, Nwandu Ukoha, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara tun a watan Oktoban 2022, ya samu dala dubu 63 da 590 ta hanyar damfara.

Ukoha ya ce wanda ake tuhumar ya kuma saci kudin wani mai suna Chinedu Ugokwe.

Ya shaida wa kotu cewa an bai wa Isah kudin ne, da nufin ya canza su zuwa Naira amma wanda ake kara bai yi ba.

Karanta Karin: Muna binciken ma’aikatun gwamnati biyu kan zargin badaƙala – EFCC

Mai gabatar da kara ya kara da cewa wanda ake kara ya kuma rike adadin kudin da ake zarginsa da damfarar su.

Sai dai lauyan wanda ake kara Emmanuel Ogbeche, ya gabatar da bukatar neman beli, sannan ya bukaci a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a hannun EFCC.

Sakamakon haka, alkalin kotun ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 5, tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here