Majalisar Wakilai ta yi alwashin bankado Dalilan da suka janyo balle gidan yarin Kuje.

Reps new 1
Reps new 1

Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Majalisar Wakilan Najeriya ta yi alkawarin bankado al’amuran da suka wakana da ya kaiga fasa gidan yarin kuje a ranar 5 ga watan Yuli wanda ake danganta zargin ga kungiyar IS da ke da’awar kafa daular Islama a yammacin Afirka (ISWAP).

Shugaban Kwamitin Tsaro da bayanan sirri na Majalisar Wakilai Sha’aban Sharada ne ya bayyana hakan yayin zaman bincike tareda jin ba’asi gameda harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.

Jaridar Solacebase ta ba da rahoton cewa a ranar 22 ga watan Yuli, Wakiln majalisa sun kafa kwamitin hadin gwiwa kan tsaro da leken asiri da kwamitoci masu alaka da tsaro don bincikar musabbabin harin da aka Kai Kuje.

Sharada, wanda shi ne shugaban kwamitin hadin gwiwa, ya tabbatar wa jama’a cewa mambobin kwamitin ba za su bar lamarin yawuce haka kawai sakaka ba batareda daukar matakan dasuka dace ba.

Ya ce majalisar za ta binciki lamarin da ya haddasa faruwar lamarin, inda ya ce za a yi kokarinatuka Dan tabbatar da samar da tsaro a cikin ginin gidan gyaran halin da kewayen sa.

Ya ce za a samar da matakan da za a kiyaye sake afkuwar lamarin anan gaba da sauran sassan kasar nan.

Ya ce majalisar za ta kuma tabbatar da bin diddigin matakan da za a bi don kare rayuka da dukiyoyin mazauna babban birnin tarayya Abuja da na daukacin Najeriya.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa kwamitin hadin guiwar zaiyi tsayin daka dan aiwatar da aikin da aka dora masa.

Ya ce an samu bayanai masu ma’ana daga manyan daraktocin ma’aikatar harkokin gwamnati da hukumar leken asiri ta kasa da sauran hukumomi dake bada bayanai ga hukumomin tsaro a Najeriya.

Kwamitin yace zai sake gayyatar shugabannin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro ciki har da wasu ministocin da suka kasa amsa gayyatar da aka yi musu a baya.

Yayin zaman tattaunawar, Jawabin Dan majalisar wakilai Osai Osai (PDP-Delta) ya bada ya tada kura, inda yace kundin tsarin mulki yabada dama a damko shugabannin tsaro da suka kasa amsa gayyatar da majalisa ta yi musu.

Ya ce mataki na gaba shi ne bayar da sammacin kama su idan har suka gaza mutunta sammacin da majalisar tayi musu don jin ba’asi.

Cikin hanzari Dan Majalisar wakilai Namdas ya sanya baki, inda ya roki majalisar da ta sake gayyatar jami’an da abin ya shafa, inda ya ce wasu daga cikinsu na iya bakin aiki, duba da irin kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here