‘Yan Bindiga a Katsina sun Kama wani Barawo tare da mika shi ga Hukuma

Bandits arrest thief 1 512x430 3
Bandits arrest thief 1 512x430 3

A wani abin da za a iya bayyana shi a matsayin gwano baya Jin warin jikinsa, wasu gungun ‘yan bindiga sun ‘kama wani dan fashi, wanda ke yin sata, a jihar Katsina.

PRNigeria ta tawaito cewa, Barawon mai matsakatan shekaru, ya kware wajen satar roduna da wunduna, daga gine-ginen da ba kowa a ciki a jihar.

An gano cewa ‘Yan bindigar sun kama mai laifin ne a lokacin da suke sintiri a kan babura.

Wani faifan bidiyo na musamman da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu ya nuna yadda ‘yan ta’addan suka yi holen barawon a gaban wani shugaban yankin.

Ko da yake ba a iya tabbatar da ranar da abin ya faru ba daga faifan bidiyon inda ‘yan fashin suka gargadi barawon game da hadarin sata.

‘Yan bindigar, wadanda a cikin faifan bidiyon dauke da manyan bindigogi, sun shaida wa shugaban al’ummar yankin da ya tabbatar da cewa an hukunta barawon kamar yadda doka ta tanada don hana wasu yin sata.

PRNigeria ta tattaro cewa ‘yan bindigar ba wai kawai sun mika barawon ga sarkin Katsina bane sai da suka tabbatar da cewa jami’an tsaro sun tafi da shi domin ya amsa tambayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here