Wata baƙuwar cuta da ake zargin cutar sankarau ce a jihar Kebbi ta kashe mutane akalla 26, a cewar gwamnatin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Alhaji Musa Ismaila, ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Talata.
“A cikin mako bakwai, muna cikin mawuyacin hali na barkewar cutar, tare da karuwar adadin masu kamuwa da ita fiye da yadda aka saba, inda take farawa da alamun cututtuka kamar zazzabi, matsanancin ciwon kai, taurin wuya, ciwon ciki, amai, gudawa da rashin son haske.
“Jimillar mutane 248 da ake zargi sun kamu tuni aka dauki samfuransu inda aka aika zuwa dakin gwaje-gwaje na Abuja don tabbatarwa.
Karin karatu: Kebbi: ‘Yan sanda sun tabbatar da kashe mutane 11 da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka yi
Ismaila ya ce an gudanar da ziyarar bayar da shawarwari ga masu ruwa da tsaki tare da hadin gwiwar hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kungiyar Likitoci Sans Frontières (MSF), da Asusun Ba da Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta saki Naira miliyan 30 don siyan magunguna da sauran kayayyakin masarufi don gudanar da ayyukan da suka dace don rage tasirinta.
Ya kuma ce an raba magunguna da sauran kayayyaki ga kananan hukumomin da abin ya shafa.
Daga nan sai kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su bi ka’idojin kiwon lafiya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga cibiyar lafiya mafi kusa domin daukar matakin da ya dace. (NAN)