Dokar Zabe: Majalisar dattawa ta dakatar da yanke hukunci zuwa watan Janairu

Senate at plenary
Senate at plenary

Majalisar dattawa ta ce sai zuwa watan Janairu za ta yanke hukunci kan kin amincewa da gyaran dokar zabe da Shugaba Muhammdu Buhari ya yi.

Majalisar dattawan ta ce matakin zai ba ta damar tuntubar majalisar wakilai da ke hutu a halin yanzu da kuma neman ra’ayin mazabarsu.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar na yau laraba a Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here