Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun Kirismeti da sabuwar shekara

6567BA6B A94B 4D34 BDC7 474D7AD7EBD1
6567BA6B A94B 4D34 BDC7 474D7AD7EBD1

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun litinin 27 da talata 28 ga watan Disamba a matsayin ranakun hutun Kirismeti.

Sai kuma ranar 3 ga watan Janairu a matsayin ranar hutun sabuwar shekarar 2022.

Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida Dakta Shuaib Belgore ya fitar yau laraba a Abuja.

Sanarwar ta ce Aregbesola ya yi kira mabiya addinin kirista da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwan kirismeti wajen yi wa kasar nan addua wajen samun ci gaba mai dorewa.

Ministan ya bukaci al’umma da su kiyaye duk wasu ka’idoji da aka gindaya domin kaucewa yaduwar cutar COVID-19.

Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati ta samar da ingantattun matakai na tsaron rayuka da dukiyoyi tare da fatan ‘yan Najeriya su marawa kokarin jami’an tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Aregbesola ya roki dukkan ‘yan kasar da su ci gaba da mai da hankali tare da bayyana kwarin gwiwa cewa shekarar 2022 za ta kasance mafi alheri a gare mu baki daya. Yana yiwa daukacin kiristoci musamman kiristoci barka da Kirsimeti da daukacin ‘yan Najeriya barka da shiga sabuwar shekara lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here