Kimanin Sanatoci 81 ne cikin 109 suka amince da ajiye matakin hukuncin da shugaba Buhari ya ɗauka na ƙin sanya hannu a sabuwar dokar zaɓe da aka yiwa kwaskwarima.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, cikin wata doguwar wasika da ya aike wa majalisun dokoki, Ya buƙaci ƴan majalisun da su tsame sashen da ke ƙoƙarin halasta aiwatar da zaɓen ƴar tinƙe yayin zaben fidda gwani kafin ya kai ga sa hannu kan dokar.
Haka kuma cikin wasiƙar shugaba Buhari, ya yi bayanin cewa rashin cikakken tsaro na daya daga cikin dalilan da ya sanya shi ƙin amincewa da ƙudurin dokar a karo na biyu.
Wasu ƴan majalisar dattawa da suka nemi a sakaye sunansu, sun labarta wa Solacebase cewa da dama daga cikin sanatocin da suka rattaba hannu, sun fito ne daga yankin Arewa maso Yammacin ƙasar nan, kuma ƴan Jam’iyyar APC ne.
“Kun ga ƴan majalisun dattawan nan da suka rattaba hannu kan amincewa da kudurin, haƙiƙa ba sa farin ciki da matakin da shugaban ƙasa ya ɗauka” Inji Sanatan
“Kuma a shirye muke mu yi abinda ya dace tunda muna da kaso mafi rinjaye a wannan karon” Inji shi
Idan za a iya tunawa dai, ƙudurin dokar da aka yiwa gyaran fuskar tare da aike wa shugaba Buhari tun a 19 ga watan jiya na Nuwamba, Zaurukan majalisun biyun suka sahale kuma aka tura wa shugaban ƙasar duk da cewa shugabannin jam’iyyar APC ba sa goyon bayan gyaran dokokin.
Rahotonni sun ce, ƙudurin dokar ba iya zaɓukan fidda gwanin kai tsaye ya tsaya ba, kudurin ya kuma ƙunshi tanadin aike wa da sakamakon zaɓuka ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC domin rage kashe kuɗaɗe lokacin zabe.













































