Farashin tumatur ya sauka sakamakon yawaitar amfani 

Tomatoes

 

Farashin tumatur ya ragu sosai a Lagos da wasu sassan Najeriya sakamakon yawaitar amfani da ake samu a lokacin girbi.

Wannan yanayi yana faruwa duk shekara daga watan Janairu zuwa Maris.

A halin yanzu, kwandon tumatur mai nauyin 50kg ana sayar da shi akan N10,000 zuwa N15,000 a wasu kasuwanni, inda a baya ya kai N140,000 zuwa N150,000 a watan Mayu 2024.

Shugaban kungiyar masu noman tumatur a Jihar Kaduna, Rabiu Zuntu, ya bayyana cewa matsalar rashin kayan ajiya da sarrafa tumatur na janyo asarar kashi 50% na amfanin gona.

Ya shawarci jama’a su ajiye tumatur ta hanyoyin gargajiya kamar markadawa da zuba a cikin kwalabe.

‘Yan kasuwa da masu saye sun yaba da wannan saukin farashi, inda wasu ke cewa lokaci ne na tanadi don gujewa tsadar tumatur a gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here