Wani mummunan hatsarin ya faru a Potiskum, Yobe, ya yi sanadin mutuwar wani matashi, mai suna Abubakar Haruna, yayin bikin kai amarya.
Lamarin, wanda ya faru a ranar Juma’a da yamma, ya sake haifar da damuwa kan halin rashin kula da kai da wasu matasa ke nuna wa yayin bukukuwa na yau da kullum a cikin al’umma.
Shaidun gani da ido sun ce wata tawagar matasa da ke kan hanyarsu ta kai amarya sun hau babura suna tukin ganganci da kuma tashin hankali ta wani yanki mai cunkoson jama’a a cikin garin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa masu hawan baburan suna tafiya ne cikin gudun wuce sa a, suna tafiya mai hadari, kuma ba su damu da masu tafiya a kafa ko sauran masu amfani da hanya ba.
Dan’uwan mamacin, Muhammad Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN).
Ya ce lamarin ya koma mummuna yayin da tawagar ta tunkaro wani yanki mai cunkoso.
“Dan’uwana yana tsaye a gefen hanya ne lokacin da daya daga cikin masu hawan babur ya buge shi da karfi a kai,” in ji shi.
Ya ce karfin bugun ya sa Abubakar ya rasa daidaito kafin ya fada cikin wata magudanar ruwa da ke kusa.
“Kafin kowa ya taimake shi, ya riga ya mutu sakamakon raunukan da ya samu,” in ji Muhammad.
Ya bayyana mutuwar a matsayin abin tausayi, wadda ta faru ba zato ba tsammani, kuma da a iya hana faruwarta. Inda ya ce “Wannan ba kawai zafi ba ne ga iyalinmu, har ila yau abu ne da bai kamata ya faru ba,” in ji shi.
Muhammad ya ce tuki cikin rashin kulawa yayin kai amarya ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a yankin, “Kowane biki yanzu yana zuwa tare da nuna kwarewar hadari kan babura,mutane marasa laifi koyaushe suna cikin hadari,” in ji shi.
Ya kira ga hukumomi a Yobe da su sanya ka’idojin tsaro masu karfi da kuma aiwatar da dokokin zirga-zirga da ke akwai.












































