Najeriya ta bai wa ‘yan Ruwanda damar shiga kasar ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 30

tinubu rwanda 680x430

Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta ce ta kammala shirye-shiryen aiwatar da manufofin shiga kasar ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 30 ga ‘yan kasar Ruwanda da ke shigowa Najeriya.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Mista Akinsola Akinlabi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a a Abuja.

Akinlabi ya ce umarnin ya biyo bayan sanarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a taron Africa CEO Forum da aka gudanar a Kigali na kasar Ruwanda.

Ya ce Shugaban ya bai wa ‘yan kasar Ruwanda damar shiga Najeriya ba tare da bizar ba ne a matsayin sakayya, kamar yadda gwamnatin Ruwanda ta bai wa ‘yan Najeriya.

Ya kuma ce karkashin wannan yarjejeniya ta hadin gwiwa, za a bai wa ‘yan kasar Ruwanda damar shiga Najeriya ba tare da biza ba na tsawon lokaci da bai wuce kwanaki 30 ba don dalilai na doka.

Duk da haka, ya lissafa dalilan da suka hada da yawon bude ido, kasuwanci da al’amuran gwamnati.

A cewarsa, duk wani dan kasar Ruwanda da ke niyyar zama a Najeriya fiye da kwanaki 30 da aka amince da su dole ne ya fitar da bizar da ta dace.

“Wannan za a yi shi ne ta ofishin jakadancin Najeriya ko babban kwamishinan da ke waje ko kuma ta hanyar shafin e-Visa na Najeriya,” in ji shi.

Mai magana da yawun hukumar shige da fice ya ce an umarci dukkan wuraren shiga kasar da su fara aiwatar da wannan manufofi nan take bisa umarnin shugaban kasa.

Ya bayyana cewa wuraren shigar sun hada da filayen jirgi, iyakokin kasa da tashoshin jiragen ruwa.

Akinlabi ya bayyana cewa wannan shiri na nuna karfin dangantakar diflomasiyya da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Ruwanda.

Mai magana da yawun NIS ya bukaci jama’a da ke bukatar karin bayani ko taimako kan manufofin da su tuntubi hukumar ta hanyoyin sadarwar da aka tabbatar.

Ya lissafa hanyoyin sadarwar a kamar X da Instagram: @nigimmigration; Facebook: @nigimmigration; lambobin cibiyar sadarwa: 09121900655, 09121556359 da 09121477092, wadanda ake samu awanni 24 kowace rana.

Ya kuma lissafa lambobin WhatsApp a matsayin 0916087800 da 09117717772. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here