‘Yan sanda sun kama wani mutum kan zargin yunkurin satar mahaifa don aikin bokanci a Katsina

Police olopa new 750x430

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum mai shekaru 50 da ake zargi da yunkurin gudanar da aikin boka da ta shafi jariri a Babban Asibitin Funtua.

Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Katsina.

Ya bayyana wanda ake zargin da sunan Sagir Muntari, wanda aka kama bayan jami’in tsaron asibitin ya ba da rahoton zargin faruwar al’amarin a cikin asibitin.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Mayu da misalin karfe 4:20 na yamma lokacin da wani ma’aikacin asibitin ya ga Muntari yana yawo cikin yanayin zargi a asibitin, lamarin da ankarar da jami’an tsaro.

“An tura Jami’an bincike nan take wurin da lamarin sannan suka kama wanda ake zargin,” in ji Sadiq-Aliyu.

Binciken farko da ‘yan sandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya shiga asibitin da niyyar samun mahaifar jariri don aikin bokanci da tsibbu.

Yayin da ‘yan sanda ke yi masa tambayoyi, wanda ake zargin, Muntari, ya amsa laifin ana kuma ci gaba da bincike.

“Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike,” in ji mai magana da yawun rudunar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here