Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane 21 sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a wasu yankuna biyu da sanyin safiyar ranar Alhamis.
Yankunan da iftila’in da ya shafa sun hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa a cikin garin Mokwa da ke karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Lamarin ya faru ne yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shafe sa’o’i ana tafkawa a ranar Alhamis.
Hukumar ta NSEMA, ta cikin wata sanarwa da babban Daraktanta Abdullahi Baba Arah ya fitar, ta ce ambaliyar ruwan ta mamaye tare da rushewar gidaje sama da 50 tare da mutanen da ke cikin su.
Dangane da wannan iftila’i, ya ce hukumar tare da hadin guiwar Majalisar karamar hukumar Mokwa, da masu ruwa da tsaki na cikin gida da kuma jajirtattun ‘yan sa kai, suna ci gaba da gudanar da aikin ceto wadanda suka ke da rai tare da lalubo gawarwakin wadanda suka rasu.
A cewarsa, a halin yanzu an ceto mutane uku da suka hada da mace daya da ‘ya’yanta guda biyu, Inda samun kulawar likitoci a babban asibitin Mokwa.













































