Kuskurene a dinga ba wa barayi mukaman ministoci – Sarki Sanusi

kano, gwamnati, rushe, masarautu, sanusi
Gwamnatin Kano ta mayar da Muhammadu Sanusi II Sarkin Kano.Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a wani taron maneman labarai da...

 

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa kan lalacewar ɗabi’u da ƙima a cikin al’ummar Najeriya.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a Channels TV, Sanusi ya nuna rashin jin daɗi ganin ana ba wa mutanen da suka yi wa ƙasa zagon ƙasa da sata mukaman gwamnati.

Ya ce al’umma na girmama dukiya fiye da gaskiya da halaye nagari, koda kuwa an san an samo ta ta hanyar haram.

Ya bayyana cewa: “Mun rasa kunya wajen jin tsoro ko ƙyama ga mutanen da suka yi sata, muna ba su ƙarin mukamai, muna barin su ci gaba da satar dukiyar jama’a.”

Sanusi ya kara da cewa yawancin shugabanni a Najeriya ba suna shiga gwamnati ne kawai don su tara dukiya.

Ya ce irin waɗannan mutane ba sa damuwa da suna ko nagarta, sai abin da suka mallaka – gidaje, jiragen sama masu zaman kansu, da biliyoyin kuɗi a asusu.

Sarkin ya jaddada cewa gaskiya, ƙwazo da tausayi ya fi dukiya muhimmanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here